Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Mista Habre ya rasu ne a asibiti yayin da yake zaman gidan yari a Senegal bisa aikata laifukan yaki da cin zarafin dan Adam.
An bayyana cewa ya rasu ne sakamakon cutar korona, kamar yadda kamfanin labarai na AFP ya ruwaito.
Habre ya kwace mulki a shekarar 1982 inda ya jagoranci kasar na shekaru 8 kafin kifar da mulkinsa a shekarar 1990 abinda ya sa shi gudun hijira zuwa kasar Senegal.
A shekarar 2016 babbar Kotu a Senagal ta yanke masa hukuncin kisa saboda laifukan cin zarafin bil adama a zamanin mulkinsa.
kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun kiyasta cewa a lokacin mulkinsa Hissene Habre, an kashe mutane akalla dubu 40.
342/